Hajiya Ladi Audu Bako, wacce mata ce ga gwamnan Kano na farko a mulkin soji (1967 zuwa 1975), kwamishinan yan sanda Marigayi Alhaji Audu Bako, ta rasu tana da shekaru 93 a Duniya, bayan rashin lafiya ta tayi wacce har ta kai ga an kwantar da ita a Asibiti.
Za’ayi jana’izar ta da misalin karfe 2:00pm na rana a wannan Rana ta Laraba (5/4/2023) a fadar masarautar Kano, kamar yadda diyar ta, Zainab Audu Bako, ta bayyana.