Home » Kebbi: Hukumar Kwastam Ta Kama Kayayyaki Na Kusan Miliyan 23

Kebbi: Hukumar Kwastam Ta Kama Kayayyaki Na Kusan Miliyan 23

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar kwastam reshen jihar Kebbi ta kama wasu kayayyaki na fasa ƙwauri da harajinsu ya kai Naira Miliyan Ashirin da uku, da dubu dari da arba’in da ɗaya, da naira dari takwas da uku a wurare daban-daban na jihar.

A cikin watanni uku da suka wuce ne, Shugaban Kwastam din, ya ce ya karbi ragamar shugabancin hukumar, inda ya bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara a fannin samun kuɗaɗen shiga,

Sannan ya bayyana cewa; a cikin watan Maris, hukumar ta samu jimillar kudi Naira Miliyan dari da arba’in da hudu, da dubu dari takwas da sittin da biyu, da naira dari uku da saba’in da biyu

Ya kuma kara da cewa, kayayyakin da aka kama sun haɗa da: Fetur lita 16, 375, katan ɗin spaghetti 210 na ƙasar waje, ƙunshi 34 na kayan sawa na hannu da kuma katan 109 na kayan zaki da dai sauransu.

Sannan hukumar ta samu sahihan bayanan sirri na ayyukan fasa ƙwauri na Fetur a gidan man AP da ke Yauri a karamar hukumar Yauri a jihar,

Inda ta tura tawagar jami’an hukumar zuwa wurin tare da kama, da kuma sake yin artabu da waɗansu da suka zo daga baya da wasu ‘yan baranda da nufin hana kwace haramtaccen man.

Amma jami’an hukumar sun tsaya tsayin daka har zuwa lokacin da aka kai ga samun agajin sojojin Nijeriya wadanda suka taimaka wajen tarwatsa masu fasa kwaurin.

Daga nan ne ya gode wa duk ’yan kasa musamman na jihar da ke taimakawa Kwastam da bayanai masu amfani wajen dakile fasakwaurin a jihar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi