‘Yan sanda a Angola sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutanen da suka fito suna zanga-zanga kan karin farashin man fetur a ƙasar.
Dubban mutane sun fantsama kan tittuna a birnin Luanda da sauran manyan birane.
Angola da ke ta biyu a arzikin man fetur a Afirka – ta zabtare kuɗin tallafin da take bayarwa a fetur a watan da ya gabata, lamarin da ya ninka farashin a gidajen mai.
‘Yan adawa da ƙungiyoyin fararan-hula sun ce an yi gaggawa wajen cire tallafin, tare da kira ga ‘yan sanda su daina amfani da ƙarfi kan masu bore.
A makon da ya gabata mutum biyar aka kashe lokacin da ‘yan sanda suka buɗe wuta kan direbobin tasi da babura da ke zanga-zanga.