Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Gombe, ta bayyana cewa an samu qaruwar sabin masu yin tazarar haihuwa a jihar, da kimanin mutane 28,561 daga watan Janairu zuwa Maris ɗin 2023.
Ko-odinetar sashin tazarar haihuwa a hukumar, Grace Mabudi ce ta bayyana hakan yayin taron rubu’i na biyu na Ƙungiyar ‘ƴan jarida masu aiki da Ƙungiyar The Challenge Initiative (TCI) kan tazarar haihuwa a jihar.
Grace ta ce “Qaruwar bata rasa nasaba da jajircewar da kafofin watsa labarai da qungiyoyin ci gaba suke yi wajen wayar da kan jama’a musamman iyalai kan mahimmancin tazarar haihuwa. Gaskiya kuna qoƙari”.
Sai dai ta yi qira ga ’ya’yan qungiyar su qara himma wajen samar da kayan da ake amfani da su wajen gudanar da wasu hanyoyin na tazarar haihuwa, wanda shi ne babban qalubalen dake fuskantar ayyukan tazarar a jihar.
A cewarta, jihar tana da wadatatun magungunan tazara, amma tana fama da qarancin kayan da ake amfani da su kamar su auduga, da sirinji, da safar hannu, filasta da sauransu, tana mai tabbatar da cewa dole sai da kayayyakin kafin a iya gudanar da wasu nau’o’in na tazarar haihuwa.