‘Yan Sandan Sun Kama Waɗanda Ake Zargi Da Cire Kan Almajiri A Adamawa
Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Adamawa ta bayyana kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani yaro Almajiri dan shekara 10 a karamar hukumar Jada.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Adamawa ta bayyana kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani yaro Almajiri dan shekara 10 a karamar hukumar Jada.
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya da ta yi suna da tabarujji da badala a jihar Kano sakamakon wulaƙanta takardar Naira.. Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira. […]
Wasu ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.
Wani ango mai suna Abba Musa da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu ciki har da ‘yar uwar amaryarsa Raihanatu Sulaiman sun rasu a hanyar tafiya daurin auren sa a kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi. Kafin ɗaurin auren ne Abba Musa da Maryam Sulaiman […]
Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA.
Kwamitin tsaron da gwamnatin jihar Kano ta kafa don magance fadace-fadacen daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma gyara tarbiyar matasa, ya kai sumame tare da kama matasa 53, a wuraren da aka samu rahotannin yan daba da masu sayar da kayan maye suna taruwa, don su fito fadan daba a cikin […]
Daga : Safiyanu Haruna Kutama Kwamishinan shiri’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ya bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba, sai dai ya ce kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncinta ne har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar. […]
Rundunar yan sandan jihar Jigawa, ta kama wani malamin makaranta da zargin da halaka Almajirinsa mai suna Bashir Ahmed, ta hanyar dukansa da Bulala saboda rashin zuwa makaranta ba tare da sanin malamin ba. kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa SP Lawan Shiisu Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aikewa da […]
Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da duk wani nau’i na tashe a fadin jihar, sakamakon yadda wasu batagarin matasa suke fakewa suna aikata laifuka. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aikewa da manema labarai a ranar […]
Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta kaddamar da shirin rabon abinci na kasa na 2025 da darajarsa ta kai Naira biliyan 16, wanda zai tallafawa ‘yan Najeriya miliyan daya da kayan abinci.