Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Tallafin Biliyan 16

Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta kaddamar da shirin rabon abinci na kasa na 2025 da darajarsa ta kai Naira biliyan 16, wanda zai tallafawa ‘yan Najeriya miliyan daya da kayan abinci.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar da aka gudanar a Jihar Kano, Shugaban Gidauniyar, Alhaji Aliko Dangote, wanda diyarsa Maryam Aliko Dangote ta wakilta, ta bayyana cewa shirin yana da burin rage radadin talauci da yunwa a wannnan lokacin.

Wannan shiri yana nuna tausayawa, hadin kai da kuma kishin al’umma. A cikin wannan mawuyacin hali da kasar ke fuskanta, muna kokarin bayar da gudunmuwa domin rage matsin rayuwa,” in ji shi.

Shirin zai fara ne a Jihar Kano, inda za a raba jakunkuna 120,000 na shinkafa ga talakawa a kananan hukumomi 44 na jihar, kafin a ci gaba da rabawa a sauran jihohin Najeriya.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya wakilta, ya jinjinawa Dangote bisa wannan gagarumin tallafi da ke nufin kawar da yunwa a kasar.

Post masu alaƙa

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano