INEC Ta Yi Tirjiya Game da Hukuncin Wata Babbar Kotu Kan Amfani da Katin Zaɓe Na Wucin-gadi
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta kasa ta ce tana shirye-shiryen ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu wanda ta bai wa waɗanda suka shigar da ƙara damar yin zaɓe da katin zaɓe na wucin-gadi.