Nijar Ta Amince da Ƙawancen Mali Domin Yaƙi da ‘Yan Ta’adda

Mali da Nijar sun amince a farkon watan nan cewa su yi aiki tare domin murƙushe ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Al-Qaeda da IS.

Sannan Shugaban ƙasar Nijar, Muhammad Bazoum ya naɗa sabon babban hafsan dakarun sojin ƙasar, daidai lokacin da Nijar ke fafutukar murƙushe ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Kawo yanzu, gwamnati ba ta yi bayani a kan dalilan maye gurbin Janar Salifou Mody da Janar Abdou Sidikou Issa ba, wanda a baya ya riƙe manyan muƙamai a ɓangaren na sojoji.

Akwai ƙungiyoyi da dama na masu iƙirarin jihadi a Nijar ciki har da Boko Haram wadda ta samo asali daga Najeriya mai maƙwabtaka.

Post masu alaƙa

Dalibai huɗu za su wakilci Najeriya a gasar Spelling Bee ta Duniya a China

Babandede Ya Taya Shettima Murnar Sake Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Ban taɓa haɗuwa da Adeyemi ba — Gbajabiamila