• Home  
  • Amurka ta kai wa Najeriya tallafin ‘kayan aikin soji’
- Babban Labari - Labarai

Amurka ta kai wa Najeriya tallafin ‘kayan aikin soji’

Rundunar sojin Amurka da ke gudanar da aikinta a nahiyar Afirka ta sanar da bai wa Najeriya kayan aiki bunƙasa yaƙi da matsalar tsaro. Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, yau Talata. Sanarwar ta ce “dakarun Amurka sun sauke muhimman kayan aikin soji ga abokan huldarmu na […]

Rundunar sojin Amurka da ke gudanar da aikinta a nahiyar Afirka ta sanar da bai wa Najeriya kayan aiki bunƙasa yaƙi da matsalar tsaro.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, yau Talata.

Sanarwar ta ce “dakarun Amurka sun sauke muhimman kayan aikin soji ga abokan huldarmu na Najeriya a Abuja.

“Wannan tallafi zai taimaka wa Najeriya a wajen ayyukanta, kuma hakan ya ƙara jaddada alaƙar tsaro da ke tsakanin mu,” a cewar sanarwar.

Haka kuma sanarwar na ƙunshe da hoton wani jirgin dakon kaya da ƙofarsa a buɗe, yayin da za a iya ganin wasu kaya jibge a kusa da jirgin.

Najeriya na fama da matsalar tsaro a yankunanta daban-daban: waɗanda suka hada da matsalar ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, da ƙungiyoyin ƴan bindiga a arewa maso gabashin ƙasar da arewa ta tsakiya, sai kuma ƴan aware a kudu maso gabashin ƙasar.

A ranar 25 ga watan Disamban 2025 ne Amurka ta ce ta kai hari kan ƴan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar IS a jihar Sokoto da ke Najeriya.

Duk da babu cikakken bayani kan tasirin harin, amma shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren “suna da ƙarfi da haɗari”.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai