Cibiyar bincike da koyar da harkokin bincike a kan karatu ta buɗe wani katafaren ɗakin karatu domin koyarwa da dawo da al’adar karatu a tsakanin ‘yan Najeriya.
Da take bayyana buɗe sabon ɗakin karatun, wanda aka sanyawa sunan “Rebecca Rhodes Reading Room” shugabar cibiyar, Farfesa Talatu Musa Garba, ta bayyana cewa Malama Rebecca wata ‘yar gwagwarmaya ce da ta tafiyar da rayuwarta a kan harkokin koyo da koyar da karatu, tun tsawon shekaru 40 da suka shuɗe.
Ɗakin karatun ya ƙunshi tarin kayan karatu waɗanda suka ƙunshi harkokin karatu na zamani da na na’ura da littattafai da sauran kayan koyar da karatu na zamani.
Shugabar Cibiyar ta bayyana cewa har yanzu ƙofar Cibiyar a buɗe take ga dukkanin waɗanda suke son haɓaka harkokin karatu, tare da samar da hanyoyi na zamani da za su taimakawa masu son haɓaka hanyoyin karatunsu.
A yanzu haka dai cibiyar tana gabatar da taronta na ƙasa domin haɓaka hanyar koyar da karatu a Najeriya