Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta amince da tsawaita wa’adin dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22.
Tun da farko hukumat ta sanar da dakatar da nuna finafinan ne sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar, sannan ta ba masu finafinan mako ɗaya su cika ƙa’idojin hukumar.
Sai dai a wata sanarwa da shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Najeriya (MOPPAN) reshen jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, ya ce an tattauna, kuma an fara samun mashalah.
“Bayan doguwar tattaunawa da shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha da wasu ma’aikatansa da wakilan Kannywood, an samu matsaya a kan:
Hukumar ta yarda ta ƙara mako ɗaya a cigaba da sakin finafinan da suke a layin fitowa don kada masu finafinan su yi asara
Za a sake zama ranar Alhamis domin sake tattaunawa domin a ƙarƙare maganar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilan MOPPAN da Abdul Amart da Nazifi Asnanic da Abubakar Bashir Maishadda da sauransu.