Daga Safiyanu Haruna Kutama
Hukumomin tsaro sun kuma kama mai garkuwa da mutane a dai-dai lokacin da yake shirin tafiya aikin Hajji a filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Sokoto.
Jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) ne suka kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi, yayin da ake tantance maniyyata domin hawa jirgin zuwa ƙasar Saudiya
An kama shi ne a safiyar ranar Litinin, washegarin da jami’an tsaro suka kama wani ɗan bindiga yana yana shirin hawa mota zuwa filin jirgin sama na Abuja domin zuwa aikin Hajji.
- An Cimma Matsaya Kan Dakatar Da Haska Fina-finai 22 A Kano
- Digiri Dan Kwatano : Majallisa Ta Amince A Ba Wa Dan Jaridar Da Ya Bankado Digirin Bogi Tsaro.
Wani babban jami’in tsaro a Sakkwato ya shaida wa Daily Trust cewa ana yiwa Sani Galadi tambayoyi kuma yana bayar da muhimman bayanai kafin a gurfanar da shi a kotu.
Da aka tambayi jami’in yadda aka yi dan bindigar ya samu tantancewa domin zuwa aikin Hajji, ya ce “sai a tambayi hukumomin da abin ya shafa”.