Home » Digiri Dan Kwatano : Majallisa Ta Amince A Ba Wa Dan Jaridar Da Ya Bankado Digirin Bogi Tsaro.

Digiri Dan Kwatano : Majallisa Ta Amince A Ba Wa Dan Jaridar Da Ya Bankado Digirin Bogi Tsaro.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da a ba wakilin jaridar Daily Nigerian ta intanet a Najeriya, Umar Audu tsaro na shekara goma saboda binciken ƙwaƙwaf da ya yi, wanda a ciki ya bankaɗo yadda ake amfani da kuɗi wajen mallakar digirin bogi daga Jamhuriyar Benin.

Binciken Mr Audu ne ya bankaɗo harƙallar mallakar kwalin digirin ta bayan fage, da kuma yadda ake amincewa da su a Najeriya a hukumance.

A zaman majalisar a ranar Litinin, ɗanmajalisa Abubakar Fulata ne ya sanar da umarnin majalisar, sannan ya yi kira da Rundunar ƴansanda da ta tsaron masu farin kaya wato NSCDC da sauran jami’an tsaro da su tabbatar da tsaron Audu.

“Muna godiya tare da yaba jajircewar Audu. Muna kira ga Ministan Harkokin Cikin Gida ya tabbatar jami’an tsaron NCDC sun ba Audu tsaro da ma ƴansanda,” in ji Fulata kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito daga NAN.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?