An dakatar da tattara sakamakon zaben gwaman na jihar Adamawa sakamakon ta da hargitsi da wasu suka a cibiyar hukumar jihar.
Mutan nan dai na ɗauke da makamai a yayin kai wannan hari kan cibiyar hukumar da ke tattara sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar da ke birnin Yola.
Majiyarmu ta shaida mana cewar tun a tsakar daren jiya ne maharan suka yi wa cibiyar tattara sakamakon zaben na gwamna kawanya tare da hana shiga ko fita daga cikinta,
Sai dai daga bisani jami’an hadin gwuiwar na ‘yan sanda da sojoji sun kawo karshen tashin hankalin.
Majiyar tamu ta kuma shaida mana cewa an kammala tattara sakamakon zaben gwamnan a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 da ke fadin jihar.
Sai dai rashin tabbatar da alkaluman ƙuri’un da aka kada a karamar hukumar Fufore inda ‘yan daba suka kwace sakamakon, wanda kuma hakan ya sanya hukumar jinkirta sanar dan takarar da ya yi nasara har izuwa yau Litinin da muke ciki.
Tuni kuma jami’an tsaro suka sake kintsawa wajen shirin ko ta kwana domin tabbatar da da tsaro.