Gwamnatin jihar Kano, ta bakin kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba, ta sanar da sanya dokar zama a gida na daga safiyar wannan rana zuwa dare.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen gwamna na jihar Kano da hukumar zaɓe ta yi tare ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Ya ce wannan mataki ne da aka ɗauka domin magance yiwuwar ɓarkewar tashe-tashen hankula a jihar.
Sai dai har izuwa yanzu al’umma na cigaba da fitowa da yawo kan tituna domin bayyana farin cikinsu game da nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu.