Gwamnatin Jihar Zamfara ta dawo da wasu malamai 103 da aka kora a baya sakamakon binciken tantance ma’aikata tare da biyan su bashin albashin watanni bakwai.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Malam Wadatau Madawaki, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon sake nazarin tantance malaman da ma’aikatars ta gudanar.
Madawaki ya ce an cire sunayen waɗannan malamai ne bisa kuskure “ko kuma ta mantuwa” a lokacin gudanar da tantancewar.
“Bayan an kammala tantancewar, mun gano cewa malamai 103 cikin waɗanda aka cire sunayensu an yi kuskure. Sun cancanci kasancewa cikin jerin malamai da aka tabbatar da su,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce bayan gano kuskuren, ma’aikatar ta rubuta wa Gwamna Dauda Lawal takarda tana neman amincewarsa a dawo da su da kuma a biya su albashin da aka dakatar.
- Ana Zargin Wani Tsohon Gwamnan Da Ɗaukar Nauyin Sojojin Da Suka Shirya Kifar Da Gwamnatin Tinubu.
- Kidan Gangin Da Aka Hana A Unguwar Sheka Yabar Baya Da Kura.
“Daga watan Janairu zuwa Yuli 2025, Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta rubuta wa Mai Girma Gwamna tana neman ya amince a dawo da waɗannan malamai 103.
“Alhamdulillah, Mai Girma Gwamna ya amince a dawo da su tare da biyan su bashin albashin watan Janairu zuwa Yuli 2025,” in ji Madawaki.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren ilimi na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tsaftace tsarin aiki da tabbatar da inganci