Wani ɗan majalisa mai suna Madami Garba Madami, mai wakiltar mazaɓar Chikun dake jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya rasu bayan kwanaki uku da rantsar da su a majalisar jiha karo ta goma.
Dan majalisar ya rasu ne a yau Asabar 17 ga watan Yuni a asibiti bayan samun kulawar likitoci.
Wani mai mukamin gargajiya a ƙaramar hukumar Chikun, Ibrahim Saleh Ardon Ardodin, ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa.
Dan majalisar ya yi fama da jinya ko da a lokacin da ake rantsar da majalisar karo ta goma a ranar 13 ga watan Yunin shekarar da muke ciki kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Inda rahotanni ke bayyana rasuwar Dan majalisar a matsayin abin alhini, musamman ga al’ummar da yake wakilta.