Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan na Shekarar 1446 Bayan Hijra a Yau Din nan.
Tashar voice of Afric VOA ta rawaito, za a fara Azumin bana a kasa mai tsarki daga gobe asabar, a matsayin 1 ga watan Ramadana .
Kafar yada labarai ta Haramain Sharifain dake kasar Saudiyya ce ta Sanar da hakan a Sahihin shafinta na Facebook da X wato Twitter.
Dama dai yau Juma’a ne 29 ga Watan sha’aban Kuma ita ranar da mai alfarma sarkin musulmi ya bada Umarnin a fara duban jinjirin watan duban wata a Nigeria.