Home » An Kama Mutane 17 Kan Shirya Wata Zanga-zanga A Kano

An Kama Mutane 17 Kan Shirya Wata Zanga-zanga A Kano

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Mujahid Wada Musa

Rundunar yan sandan jihar Kano tare hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi karin haske kan dalilin rufe titin zuwa gidan gwamnatin jihar, sakamakon samun bayan sirri da hukumomin suka Yi na gungun wasu mutane da suke yunkurin gudanar da Zanga-zanga don tayar da hankalunan al’umma.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai, a yau Laraba ya ce , sun kama mutane 17 da ake zargin Yan Daba ne, kuma yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike.

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa rundunar taja kunnen dukkan masu yunkurin aikata abunda da zai haifar da rikici ko razanarwa da su kaucewa yin hakan , domin duk Wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Sanarwar ta ce an Yi hahan ne don tabbatar da tsaro da kuma kare rayukan al’umma da dukiyoyin su, shi yasa aka baza jami’an tsaron kuma al’umma kwantar da hankalin su.

Da safiyar yau aka ga tarin jami’an tsaron sun rufe titin zuwa gidan gwamnatin Kano kusa da gidan sarki na Nasarawa, Inda sarki na 15 yake zaune da kuma hanyar zuwa majalissar dokokin jihar.

Tun lokacin da aka fara rikicin masarauta ba a taba ganin tarin jami’an tsaro masu yawa kamar haka akan titin ba.

Kwamishinan yan sandan jihar Salman Dogo Garba, ya godewa al’ummar jihar Kano, bisa goyon baya da hadin kan da suke ba wa rundunar, Inda ya shawarce su a duk lokacin da suka ga Wani Abu da basu amince da shi ba , su gaggauta sanarwa a ofishin yan sanda Mafi kusa don daukar matakin da ya dace.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?