Rundunar Operation Haɗin Kai ta Sojin Nijeriya ta sanar da gano wani wuri da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ke ɓoye man fetur, magunguna da sauran kayayyakin aikinsu a ƙarƙashin ƙasa.
Samun wannan nasarar na zuwa ne bayan jerin samamen da dakarun rundunar Operation Desert Sanity suka kai a yankunan Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno.
Bayanai sun nuna cewa an kai samamen ne bayan hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka kai a ranar Lahadi a Chilaria, Garin Faruk da Abirma, inda dakarun suka yi nasarar daƙile hare-haren, ciki har da waɗanda aka kai da jirage marasa matuƙa.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Kai, Laftanal Kanal Uba Sani, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce farmakin ya yi sanadin lalata sansanonin ’yan ta’adda da dama, wanda kuma ya haifar wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP asara mai yawa.
A cewarsa, a ranar Lahadi 18 ga Janairu, 2026, dakarun sun kai hare-hare bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka kutsa maɓoyar ’yan ta’adda a Chilaria, Garin Faruk da Abirma.
Laftanal Kanal Uba Sani ya ƙara da cewa dakarun sun samu cikakken goyon bayan Sojin Sama na Operation Hadin Kai, waɗanda suka bayar da bayanan sirri, sa ido daga sama da kuma daƙile duk wani taimako da mayaƙan za su iya samu.
Ya ce bayan kammala farmakin, sojoji sun gano harsasai, wayoyin sadarwa, tutocin Boko Haram, man dizal, magunguna masu yawa, buhunan hatsi, a-kori-kura, da kuma wurin ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa, tare da wasu kayayyaki da dama.
