Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Najeriya a Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, ta ce ta ceto mutane sama da 47, akasarinsu mata da yara, daga hannun ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno.
Jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Maiduguri.
Ya ce an ceto mutanen ne a yankin Kangarwa, ƙaramar hukumar Kukawa, ranar 20 ga Yuni 2026, yayin wani samame da sojoji suka ƙaddamar ta ƙasa da sama kan sansanonin ISWAP a yankin tafkin Chadi.
A cewarsa, ceton ya biyo bayan ƙara matsin lamba da sojoji suka yi kan wuraren da ‘yan ta’addan suke, lamarin da ya tilasta wa mayakan ISWAP barin matsugunansu cikin rudani, wanda ya ba mutanen da aka tsare damar tserewa.
Goni ya ce wannan farmakin wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin Operation Hadin Kai na rusa maboyar ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ƙara da cewa mutanen da aka ceto suna samun kulawar lafiya a wani wuri mai tsaro, yayin da hukumomin jin ƙai ke shirya taimako domin gyara musu halin da suke ciki da kuma mayar da su cikin al’umma.

