• Home  
  • An Hana Sanata Natasha Da Takwaranta Akpabio Ganawa Da ‘Yan Jarida 
- Babban Labari - Labarai

An Hana Sanata Natasha Da Takwaranta Akpabio Ganawa Da ‘Yan Jarida 

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa dakatacciyar sanatar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio yin hira da ‘yan jarida tun da ’yar majalisar ta shigar da ƙara kotu.

Babbar Kotun Tarayya da ke a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa dakatacciyar sanatar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio yin hira da ‘yan jarida tun da ’yar majalisar ta shigar da ƙara kotu.

Wannan hukunci ya biyo bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi na cewa Natasha na ziyartar gidajen talabijin tana tattaunawa tana yin hira akan batun, duk da cewa maganar na gaban kotu.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a.

Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da aka ba izinin tattauna da manema labarai dangane da maganar.

Mai Shari’a Nyako ta yanke wannan hukunci ne bayan da A ranar Alhamis babban alƙalin kotun, Mai shari’a John Tsoho, ya mayar da shari’ar ga gareta

Binta Nyako ta ce, “Bai kamata a yi hira da manema labarai daga kowane ɓangare da lauyoyi dangane da batun wannan lamari ba, babu batun yaɗa labarai kai tsaye ko yaɗa labarai kan lamarin.

“Bai kamata a yi hira da gidan talabiji ba game da wannan batu. ” in ji mai shari’a Nyako.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai