Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama wani sanda da aka gani a bidiyo yana cin zarafin wani mai mota.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya CSP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter. Ya ce an kama dan sandan da sauran abokan aikinsa biyu da suke tare a wurin da lamarin ya faru.
Dama tun kafin a kama ‘yan sandan, sai da rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Ribas ta bayar da umarnin ganowa da kuma kamo dan sandan da aka gani a bidiyon.
SP Grace Iringe-Koko wadda ita ce mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Ribas, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Okon Effiong da kansa ya bayar da umarnin kama wanda ake zargin.
Lamarin dai ya faru ne a kwanar Elibrade da ke Karamar Hukumar Emohua a Jihar Ribas.
A cikin bidiyon, an ga dan sandan ya doki mutumin da sanda sa’annan ya rinka zabga masa mari.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Ribas ya tabbatar da cewa za a yi bincike kan dan sandan da ake zargi bisa tsarin dokokin gudanarwa na ‘yan sandan Nijeriya, kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
Haka kuma ya bukaci jama’a da su rinka kai kara kan cin zarafi ko take hakkin bil adama.