• Home  
  • An Kama Mace Cikin Masu Kwacen Baburan Adaidaita Sahu A Kano
- Babban Labari - Labarai

An Kama Mace Cikin Masu Kwacen Baburan Adaidaita Sahu A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutane 4 wadanda ake zargi da aikata laifukan kwacen baburan adaidaita sahu, cikinsu harda wata mace yar asalin jihar Bauchi. Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Hussaini Abudullahi , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai […]

Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutane 4 wadanda ake zargi da aikata laifukan kwacen baburan adaidaita sahu, cikinsu harda wata mace yar asalin jihar Bauchi.

Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Hussaini Abudullahi , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce wadanda ake zargin, Auwal Mohammed mai shekaru 30 mazaunin unguwar Hotoro da kuma Maryam Ibrahim mai shekaru 25 yar asalin jihar Bauchi, sun tare wani matukin adaidaita sahu mai suna Shu’aibu Aliyu, inda suka kwace masa babur dinsa, a karamar hukumar Kura ta jihar Kano.

Bayan samun faruwar lamarin ne aka tura tawagar jami’an yan sanda, inda bincikensu ya gano wadanda ake zargin da kuma masu siyan baburan satar da suka hada da Muhammad Tujudden ma zaunin Kundila da kuma Suleiman Lawan wanda akafi sani da Aljan dan unguwar Sheka.

DSP Hussaini Abdullahi, ya ce zuwa yanzu rundunar ta kwato baburan sata guda 6 daga wajen wadanda ake zargi da aikata muggun laifi, inda ya tabbatar da cewa da zarar an kamala gudnaar da bincike za su fuskanci hukunci daidai da laifukan da ake zarginsu da aikaata wa.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa rundunar zata ci gaba da jijircewa don yaki da masu aikata laifuka tare da kare rayukan alúmma da kuma dukiyoyinsu

Sannnan rundunar yan sandan ta yi kira ga alúmma da su zama masu sanya ido kan irin wadanda mutane a kowanne lokaci.

A karshe rundunar ta ce duk wanda yasan an sace masa babur din adaidaita sahunsa ya garzaya shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai don bincika wa

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000