Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba.
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba.
Kwamandan NDLEA na jihar, John Anteyi, yayin zantawarsa da Aminiya a Kalaba, ya ce ababen zargin sun yi iƙirarin cewa tabar wiwin wadda nauyinta ya kai tan 4.706, ta wani mutum ce da suke zaman haya a daya daga cikin dakunan gidansa.
Ma’auratan sun shaida wa ’yan sandan cewa ba su da masaniyar harkar da mutumin yake yi wanda ba a samu nasarar cafke shi ba a gidan.
Itam Onun, mai kimanin shekara 52, ta musanta cewa tabar wiwin ta su ce, inda ta ce: “Ba mu san komai ba. Shi ne mai gidan.
- Kotu Ta Yankewa Mai Tangaran Hukunci Bayan Samun Sa Da Laifin Kai Hare-Hare A Ofisoshin Yan Sandan Kano A Shekarar 2012
- ‘Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi Duk Musulmai Ne
“Mu dai haya muka karɓa a wurinsa kan naira dubu 50, ba mu san irin wannan harkar yake yi ba. Shi ya kawo kayansa ya ajiye amma ga shi an kama mu kan wannan zargin.”
Kwamandan ya ce kawo yanzu dai hukumar tana ci gaba da bincike domin gano ainihin mallakin kayan.
Kazalika, Anteyi ya jaddada cewa wannan samame na cikin yunƙurin da shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ke jagoranta na yaƙar miyagun ƙwayoyi da masu safarar su a fadin ƙasar.
