• Home  
  • An Kama Mutane 9 Bayan Rikici Ya Ɓarke Kan Kisan Ɗan Acaɓa a Garko
- Babban Labari - Labarai

An Kama Mutane 9 Bayan Rikici Ya Ɓarke Kan Kisan Ɗan Acaɓa a Garko

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta fara cikakken bincike kan zargin kisan wani ɗan acaɓa da aka yi a karamar hukumar Garko, da kuma rikicin da ya biyo bayan kama waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta fara cikakken bincike kan zargin kisan wani ɗan acaɓa da aka yi a karamar hukumar Garko, da kuma rikicin da ya biyo bayan kama waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Rundunar ta bayyana cewa a ranar 5 ga Satumba, jami’an ’yan sanda daga Wudil sun kama mutum uku da ake zargi da hannu a kisan, suka kuma kai su ofishin ’yan sanda na Garko domin ci gaba da bincike. Amma daga baya jama’a suka taru suka kai hari ofishin, suna zanga-zangar mutuwar wanda aka kashe tare da ƙoƙarin kashe waɗanda ake zargi.

Masu zanga-zangar, waɗanda ke dauke da sanduna da duwatsu, sun mamaye jami’an tsaro a ofishin.

Yayi rikicin, an ƙona motar sintiri ta ofishin, an kuma lalata wasu motoci guda uku mallakin Hisbah da karamar hukumar Garko, sannan an farfasa tagogin ginin ofishin.

Rundunar ta tabbatar da cewa jami’anta uku sun jikkata, kuma tuni suna asibitin Wudil inda ake ba su magani.

Haka kuma, yayin tarzomar, tayar da aka cinnawa wuta ta yi bindiga, ta make ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar shi, yayin da wasu uku suka samu raunuka.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce sun ɗauki matakin gaggawa inda ya tura jami’an tsaro da kuma samun tattaunawa da shugabannin al’ummar yankin.

Rundunar ta gargadi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, domin hakan na barazana ga zaman lafiya. Ta buƙaci mutane su rika kai korafe-korafensu ga hukumomi ta hanyar doka, ba wai su rika ɗaukar fansa ba.

Bakori ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa ’yan sanda za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da adalci. Ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma hada kai da jami’an tsaro.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai