An Kammala Musabukar Alkur’ani Mai Girma Tsakanin Hukumomin Tsaron Jihar Kano

An kammala musabakar alkur’ani mai girma da aka shirya tsakanin hukumomin tsaron jihar Kano, wanda rundunar yan sandan jihar ta shirya da aka shafe kwanaki ana yi.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Adamu Bakori ya bayyana cewa, wannan karatun alkur’ani da aka yi sun yi tawassali dashi bisa halin da ake ciki na rashin tsaro, a wasu wurare a jihar Kano da kuma kasa da nufin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

CP Bakori , ya ce a matsayinsu na jami’an tsaro a kowanne lokaci kansu a hade yake, kuma sun sake haduwa wuri daya wajen yin musabakar karatun alkur’ani mai girma.

Ya kara da cewa shi aikin tsaro dole ne sai an samu hadin kan jama’a domin idan babu hadin kansu baya yiwuwa kuma kullum yana shiga lungu da sako don samun hadin kan jama’a.

Babban limamin masallacin juma’a na shelkwatar rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdulkadir Haruna, ya bayyana godaiyarsa bisa nasarar da aka samu wajen shirya musabakar da kuma kammalata lafiya.

Daya daga cikin alkalan musabakar, Shiek Mudassir Adam Shu’aibu, ya bayyana cewa duk lokacin da dantakara ya zo ya zauna sun afara duba tulawarsa, domini dan yana karatu ya samu kuskure za a nuna masa alama.

Haka zalika ya ce ana kuma duba tajawidin mai karatun, da kuma irin shigarsa harma da muryarsa.

SP Habib Yunus Abdussalm , shi ne jami’in dan sandan da ya zo na daya a Izufi 20, ya bayyana jin dadinsa tare da cewa hakan ya kara masa kwarin gwiwa anan gaba.

Musabakar an shiryata Tsakanin hukumomin tsaron jihar da suka hada da yan sanda, sojoji, NDLEA, hukumar shigi da fici, Civil Defense, hukumar gidan gyaran hali da kwastam da dai sauransu.

Jami’an 41 daga hukumomin tsaro suka shiga musabakar, inda aka bawa wadanda suka yi nasara kyautuka da shaidar karramawa cikinsu harda manyan bakin da suka halacci taron kammala musabakar da aka gudanar a shelkwatar rundunar yan sandan jihar Kano.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *