Gwamnatin jihar Kano zata gudanar da karatunn alkur’ani mai girma da addu’o’I na musamman domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin kwamishinan addinai, Sheik Ahmad Tijjani Auwal , ne ya bayyana hakan yayin kammala musabakar alkur’ani mai girma tsakanin hukumomin tsaro, wanda rundunar yan sandan jihar Kano ta shirya.
Sheik Ahmad Tijjani, ya ce gwamnan jihar ne ya amince da hakan kuma shirye-shirye sun yin isa, saboda barazanar rashin tsaro da ake fuskanta a wasu kananan hukumomin Kano.
- Tinubu Ya Miƙa Sunan Dambazau A Matsayin Ambasada
- Tinubu ya rantsar da Chris Musa ministan tsaron Najeriya
Ya kara da duk da shirin da suke yi, amma jami’an yan sanda sun bude musu da musabakar karatun alkur’ani, kuma za dinga yin addu’o’in da karatun alkur’anin a ranakun Juma’a da Asabar domin samun dawamanmen zaman lafiya a Kano.
Musabakar an shiryata Tsakanin hukumomin tsaron jihar da suka hada da yan sanda, sojoji, NDLEA, hukumar shigi da fici, Civil Defense, hukumar gidan gyaran hali da kwastam da dai sauransu.
Jami’an 41 daga hukumomin tsaro suka shiga musabakar, inda aka bawa wadanda suka yi nasara kyautuka da shaidar karramawa cikinsu harda manyan bakin da suka halacci taron kammala musabakar da aka gudanar a shelkwatar rundunar yan sandan jihar Kano.
