Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, NOA, ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar Malam Lanre Issa Onilu, ta samu Lambar Yabo ta Kwarewa a Gyaran Ɗabi’u da Gina Ƙasa.
Cibiyar Centre for Positive Value Reorientation and Advocacy ce ta bayar da lambar yabon a yayin ƙaddamar da littafinta “Paradise at a Crossroads,” a NBA Hall, Ilorin.
An ba wa NOA lambar yabon ne bisa rawar da take takawa wajen wayar da kan al’umma, ƙarfafa kishin ƙasa, da bunƙasa kyawawan ɗabi’u.
Da yake miƙa lambar, Comrade Abdulwaheed Onikanhun ya yaba da jajircewar hukumar.
Da yake karɓa, Malam Lanre Issa Onilu ya nuna godiya, tare da sadaukar da lambar yabon ga ma’aikatan NOA a faɗin ƙasar, yana mai cewa hakan zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gina Najeriya mai haɗin kai da ci gaba.

