Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna damuwa cewa ba a mutunta dokokin ƙasa da ƙasa ba kan abin da Amurka ta aikata a Venezuela.
António Guterres ya bayyana haka ne a wani sako da aka karanta a taron gaggawa da majalisar ta kira kan batun na Venezuela.
“Abin damuwa ne matuka kan rashin mutunta dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela.
“Lamarin zai iya janyo rashin daidaito a ƙasar, tasiri mara kyau a yankin da kuma yadda batun zai iya sauya yanayin dangantaka tsakanin ƙasashe,” in ji Guterres.
