An kashe makiyaya 50, an sace shanu sama da 200,000 a Kaduna — MACBAN

Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN), ta ce an yi asarar shanu sama da 200,000 a Jihar Kaduna sakamakon satar shanu da matsalolin tsaro tun daga watan Janairun 2026.

Shugaban MACBAN na jihar, Alhaji Abdulhamid Musa, ya kuma ce an kashe sama da mambobin ƙungiyar 50 a tsawon wannan lokaci.

Musa, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan matsalolin tsaro da suka shafi makiyaya da masu kiwon shanu a Kaduna.

Ya ce an samu nasarar ƙwato wasu daga cikin shanun da aka sace a baya-bayan nan, har da wasu da aka gano a Jihar Legas.

Ya ce ana ƙoƙarin mayar da dabbobin ga mamallakansu.

A cewarsa, wasu daga cikin mambobin MACBAN da aka kashe sun rasu ne sakamakon rikicin manoma da kuma hare-haren ’yan bindiga.

Ya ce yankunan da aka fi samun rahotannin asarar dabbobi sun haɗa da Kachia, Chikun, Kagarko, Giwa, Igabi, Jama’a, Kaura, Sanga, Jaba, Kudan, Makarfi, Lere, Zangon-Kataf da Kauru.

Musa, ya ce shanu ba dukiya ce kawai ga makiyaya ba, domin su ne tushen rayuwarsu kuma dukiyar da suke gada iyaye da kakanni.

Post masu alaƙa

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa