Kaduna

Malaman KASU kimanin 200 ne suka bar jami’ar – ASUU

ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) reshen jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta ce malaman jami’ar kimanin 200, ciki har da furofesoshi ne suka bar jami’ar sakamakon rashin kyawun yanayin aiki da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta ƙulla da ASUU a 2025. Shugaban ASUU-KASU, Dakta Abubakar Abdullahi, ya bayyana haka a wani […]

Read more

Kotu ta ba belin mahaifi na – Bello El-Rufai

Dan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa Kotun Tarayya da ke jihar ta bayar da belin mahaifinsa. Daily Trust ta rawaito cewa a cewar dan majalisar, wanda ke cikin kotun lokacin zaman yayin da aka hana ‘yan jarida shiga, su na ƙoƙarin cika sharuddan belin da kotun […]

Read more

El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhumomin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa. An gurfanar da El-rufai ne kan laifuka da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara, da bai wa […]

Read more

Kotu ta ɗage sauraron buƙatar bada belin El-Rufai

Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026. An ɗauki wannan matakin ne bayan zaman kotun na ranar Talata, inda ɓangaren masu ƙara da masu kare kai suka gabatar da hujjoji. A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci […]

Read more

An Kammala Kilomita 39 A Titin Abuja-Kaduna-Kano – Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta ce an kammala kilomita 39 a ɓangarori daban-daban na titin Abuja–Kaduna–Kano da ake ci gaba da yi. Ƙaramin ministan ayyuka na Najeriya Barista Bello Goronyo ne ya bayyana haka, inda ya ce gwamnatin ƙasar na sa ido sosai kan yadda kamfanin da ke kwangilar, Infiouest International Limited ke gudanar a aikin domin […]

Read more