• Home  
  • An Naɗa David Mark A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC
- Babban Labari - Labarai

An Naɗa David Mark A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC

Ƙusoshin adawa a Najeriya sun bayyana tsohon shugaban Majalisar Dattijan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wadda suka amince da ita a matsayin jam’iyyar haɗaka. Ƴan adawar sun ɗauki wannan mataki ne a taron da suka gudanarwa a Abuja, babban birnin Najeriya. A jerin tattaunawar da suka gudanar na baya-bayan […]

Ƙusoshin adawa a Najeriya sun bayyana tsohon shugaban Majalisar Dattijan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wadda suka amince da ita a matsayin jam’iyyar haɗaka.

Ƴan adawar sun ɗauki wannan mataki ne a taron da suka gudanarwa a Abuja, babban birnin Najeriya.

A jerin tattaunawar da suka gudanar na baya-bayan nan manyan masu adawa da gwamnatin ƙasar sun amince da ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita domin ƙalubalantar shugaban ƙasar Bola Tinubu a babban zaɓe na shekarar 2027.

A wajen taron na yau Laraba an samu halartar manyan ƴan adawa da suka hada da Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufa’i da sauran su.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai