An rantsar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun wa’adi na biyu

An rantsar da Sanata Ademola Adeleke, wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Osun.

An yi bikin rantsuwar ne a ranar Juma’a, inda alkalin alkalai na jihar Osun, mai shari’a Adepele Ojo ta jagoranci rantsar da gwamnan a filin wasa na Osogbo City Stadium, tare da mataimakinsa, Yarima Kola Adewusi.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa wajen bikin, a madadin shugaba Bola Tinubu.

A cikin jawabin da ya gabatar bayan rantsuwar kama aiki, Adeleke ya bayyana sake zaɓensa a matsayin “nasarar muradin al’umma”.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan faɗaɗa ayyukan more rayuwa, bunƙasa masana’antu, sauya fasalin noma, bunƙasa tattalin arzikin zamani, yawon buɗe ido, da kuma ci gaban matasa da mata a wa’adinsa na biyu.

Gwamnan ya yi alƙawarin sauya tattalin arzikin jihar daga wanda ya dogara da ma’aikatan gwamnati zuwa cibiyar masana’antu.

Post masu alaƙa

Yadda Kwankwaso ya sa na yi rantsuwar komawa APC – Abba Kabir

2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa

2027: NDC ta zargi APC da gwamnatin Kano da shirin yin magudi ta tsarin tattara sakamakon zabe na INEC