Jam’iyyar NDC a Jihar Kano ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da gwamnatin jihar da kulla makarkashiyar yin amfani da tsarin Coalition Support and Result Verification System (CSRVS) wajen magudin zaben 2027.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar na shirin yin amfani da tsarin wajen shigar da kuri’un bogi a rumfunan zabe daban-daban domin bai wa APC damar samun galaba a zaben.
Daraktan yakin neman zaben NDC a Kano, Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taron manema labarai a ofishin yakin neman zaben jam’iyyar da ke Kano.
Sagagi ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da bincike domin gano sahihancin zargin, musamman kan zargin hannu da ake yi wa sashen adana takardu da Bincike na fadar Gwamnatin Kano.
“Mun samu rahotanni masu karfi cewa jam’iyya mai mulki a jihar na kokarin yin amfani da tsarin CSRVS wajen shigar da kuri’un bogi a kowace rumfar zabe domin samun gagarumar galaba.
“Muna kira ga INEC da ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin wannan zargi,” in ji shi.
Sai dai ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar cewa NDC za ta amince da duk wani zabe da aka gudanar cikin gaskiya, adalci da kuma gaskiya.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta gudanar da yakin neman zabe bisa batutuwan da suka shafi al’umma, ba tare da tashin hankali, barazana ko amfani da ‘yan daba ba.
“Za mu gudanar da yakin neman zabe bisa muhimman batutuwan da suka shafi al’umma, ba tare da tashin hankali, husuma ko daba ba. Za mu gudanar da komai cikin tsafta da lumana,” in ji shi.
Haka kuma, daraktan yakin neman zaben ya zargi gwamnatin Kano da gaza cika muradun al’ummar jihar, duk da cewa su ne suka taimaka mata ta hau mulki a shekarar 2023.
Ya ce gwamnatin ta gaza samar da ingantaccen sauyi a bangaren ilimi, yana mai nuni da karancin ababen more rayuwa, cunkoson dalibai a azuzuwa da kuma rashin tsafta a wasu makarantun sakandare, musamman na mata.
Sagagi ya kuma yi watsi da ikirarin gwamnatin jihar na cewa ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alkawarin da ta dauka, yana mai cewa ikirarin ba gaskiya, domin babu isassun hujjojin da ke nuna tasirinsa ga rayuwar al’umma.
Ya kara da zargin gwamnatin da cin amanar tafiyar siyasar da ta kai ta kan mulki, bayan da ta kulla alaka da wasu da a baya suke adawa da ita.
Sai dai ya ce NDC ta kuduri aniyar kayar da APC a zabukan da ke tafe, inda ya bukaci mambobin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar su hada kai wajen ganin sun tabbatar da nasarar dan takararta na gwamna, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo