An rantsar da sabbin shugabannin Ƙungiyar ƴankasuwa, masana’antu, ma’adanai da harkokin noma ta KACCIMA da yammacin yau alhamis a harabar cibiyar da ke Cibiyar Kasuwanci anan ciyar kano.
Hakan ya biyo bayan sabun fahinta da akai a tsakanin bangarori da ke da takaddama akan sha’anin zaben shugabannin kungiyar, wanda ya hana aiwatar da zaɓen a jiha Laraba.