Kungiyar kwallon kafa ta rundunar yan sandan jahar Kano wato CP Boys ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta matasa da tubabbun yan daba dake jahar Kano inda suka tashi kunnen doki kowannen su na da ci daya.
Kwamishinan yan sandan jahar kano muhammad husain gumel ya bayyana cewar , ba kodayaushe ne jami’an tsaro ke amfani da makami wajen samar da tsaro ba , akan yi amfani da dabaru iri-iri wajen wanzar da zaman lafiya cikin al’umma.
![](https://muhasatvr.ng/wp-content/uploads/2023/08/PHOTO-2023-08-03-16-37-04-1024x768.jpg)
A wani salo na wanzar da zaman lafiya tare da inganta rayuwar matasa a jahar kano kwamishinan yan sandan jahar kano muhammad husaini gumel ya jagoranci wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta rundunar yan sanda wato cp boys da kuma tubabbun masu laifi wato yan daba a filin wasa na sani abacha dake kofar mata.
CP Muhammad Husaini Gumel ya bayyana cewar ba ko yaushe jami’an tsaro ke amfani da makamai wajen wanzar da zamman lafiya ba, akan yi amfani da salo ko dabaru wajen cimma burin hakan.
![Kungiyar kwallon kafa ta rundunar yan sandan jahar Kano wato CP Boys ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta matasa da tubabbun yan daba dake jahar Kano inda suka tashi kunnen doki kowannen su na da ci daya.](https://muhasatvr.ng/wp-content/uploads/2023/08/PHOTO-2023-08-03-16-37-04-1.jpg)
Kwamishinan yace rage tsangwama da kuma tsana ga matasan da suka ajiye makaman su, suka daina mummunar dabi’ar nan ta daba, zai tamaka wajen inganta rayuwarsu tare da wanzar da zaman lafiya.
Wasan kwallon kafar dai ya samu halartar manyan jami’an tsaro da kuma masu sarauta da sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a fadin jahar kano, inda aka tashi wasan da ci daya daya daga kowanne bangaren yan wasan.