A yau, 29 ga watan Mayun shekarar nan, an gudanar da rantsuwar Shugaba Ƙasa Ahmad Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shattima a wurin taro na Eagle Square da ke Abuja.
Haka shi ma Sanata Kashim Shettima Tsohon gwanan jihar Borno wanda ya zama sabon mataimakin shugaban ƙasa, ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin mataimakin shugaban ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya gindaya.
A bisa al’ada, ana sa ran zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai bayyana nadin wasu muƙamai uku na farko jim kadan bayan rantsar shi da babban jojin ƙasar, Mai shari’a Olukayode Ariwoola ya yi.
Wadannan nade-nade na gaggawa na da matukar muhimmanci domin tabbatar da gudanar da ayyukan gwamnati cikin sauki yayin da za a jira wasu nade-naden da ke bukatar amincewar majalisar dokokin kasar nan.
Muhimman nade-naden uku su ne: Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da Shugaban ma’aikata da mai magana da yawun shugaban ƙasa.
Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ke sa ido tare da daidaita yadda ake aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya. Har ila yau, ofishin na aiki a matsayin cibiyar ba da shawara ga fadar shugaban kasa; yana tafiyarwa da tsara manufofi, daidaitawa, da aiwatarwa; da kuma sanya ido kan Ma’aikatun Tarayya, Cibiyoyi da Hukumomi.