Yau, 29 ga watan Mayu wannan shekarar nan ne ake gudanar da bikin rantasar da shugaban ƙasa da kuma gwamnoni da dama a Najeriya, inda aka rantsar da Injiniya Abba kabir Yusuf a matsayin sabon gwamnan Jihar kano, a bikin da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a birnin Kano.
An rantsar da shi tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar NNPP ne sanye da fararen kaya da jajayen huluna ga maza yayin da mata ke sanye da jajayen dan-kwali ko mayafi ko hijabi a wurin taron.
Sarakunan jihar ta Kano da jagorori da kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ta NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran manyan baki ne suka halarci waurin bikin taron.
Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya yi nasara ne a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris inda ya kayar da dan takarar jam’iyya mai mulki, na APC, Nasiru Yusuf Gawuna.
Tun a Jiya ne sabon gwamnan ya karɓi mulki daga hannun tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abudullahi Umar Ganduje wanda ya bayar da uzuri na zuwa taron rantsar da Tinubu a matsayin dalilin da zai hana shi halartar rantsuwa da aka yi a yau.
Sabon Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif ya bayyana cewa, sun karbi kundin mulkin jihar Kano Mai dauke da bashin fiye da Biliyan 240.
Sai dai sabon gwamnan, ya sha alwashin binciko yadda aka yi Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ciyo bashin da kuma yadda aka tafiyar da dimbin bashin.
Gwamnan jihar Kano wanda aka rantsar a yau Litinin 29 ga watan Mayun 2023 Engr. a filin wasa na Sani Abacha ya gabatar da jawabinsa cikin harshen turanci, inda ya godewa al’ummar jihar Kano bisa jajircewarsu wajen zabarsa tare da kyautata masa zato.
Wakilin mu a fadar Gwamnatin Kano ya ruwaito cewar bayan karbar kundin mulki, Tawagar Gwamna sun zarce zuwa Filin wasa na Sani Abacha stadium da ke Kofar Mata a nan Kano inda za a rantsar da su.