Gwamnan kano mai jiran gado abba kabir yusuf ya gayyaci muhammadu sanusi ii bikin rantsar da shi a kano.
za a yi bikin ne ranar 29 ga mayu a filin wasa na sani abacha a kano.
“Zawa wajen bikin ba wai zai kayatar ba ne kawai amma zai kasance muhimmin cigaba da goyon baya gare mu,” kamar yadda gwamnan mai jiran gado abba kabir yusuf ya bayyana a cikin takardar gayyata da ke ɗauke da sa hannunsa.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, kakakin gwamnan kano mai jiran gado, ne ya sheda wa manema labarai cewa ba wai Muhammadu Sanusi II kawai aka gayyata bikin rantsar da sabon gwamnan na kano ba, an kuma gayyaci sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyarsu da Aliko Dangote da Abdul Samad Isyaka Rabiu da wasu manyan mutane na Najeriya da ƙasashen waje.