Home » An Sace Mara Lafiya A Asibitin Dawanau 

An Sace Mara Lafiya A Asibitin Dawanau 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun kai hari Asibitin masu larurar ƙwaƙwalwa dake Dawanau a jihar Kano inda suka sace wata mata mai shekaru 60

Zagazola Makama shahararren mai bada labaran ta’addanci da manyan laifukan ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce an Talatu Ali mai shekaru 60 a asibitin masu larurar ƙwaƙwalwa na dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

Ya ce dattijiwar da aka sace ta tana zaman jiran kulawar likitoci a asibitin ne kafin wannan mummunan lamarin ya faru da ita.

Zagazola Makama, yace ɗan matar da yar uwarta ne suka kaita asibitin daga kauyen yar gaya na karamar hukumar Dawakin Kudu, a ranar 19 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:30, na safiya don ganin likita.

Yan uwan matar sun neme ta sun rasa a lokacin da take kan layin ganin likita.

Iyalan nata sun yi duk mai yiwuwa amma basu ganta ba, wanda hakan yasa suka kai rahoto ofishin yan sanda na Dawanau.

Sai dai kawo lokacin haɗa wannan rahoto Banu samu jin ta bakin hukumar asibitin ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?