Daga: Fatima Muhammad Adam
Majalisar Malamai Ta Jihar Kano Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masallacin Sheikh Bin Uthman (Sahaba) Dake Kundila Karamar Hukumar Tarauni A Jihar Kano.
Shugaban majalisar malamai ta Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa bayan zama da dukkanin ɓangarorin da danbarwar sabon Masallacin Sahaba dake Kundila, majalisar ta yanke hukunci na ƙarshe a kan dambarwar.
”Mun yanke hukuncin Sheikh Muhammad Bn Othman zai koma Masallacin da na Sahaba, shi kuma Mai Kifi da sauran mutanensa za su cigaba da riƙe na su Masallacin na Jami’urrahman.”
- Kano Da Abuja Sun Sami Tallafin Dabino Tan 100 Daga Saudiyya
- UNICEF Zai Ba Najeriya kwalabe Miliyan 3 Na Maganin Inganta Lafiyar Masu Ciki
Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakamakon zaman da suka yi ga manema labarai a Kano.
Ya ce Sheikh Muhammad Bin Othman ya amince zai cigaba da jagorantar Sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba dake Kundila, yayin da su kuma su Mai Kifi za su cigaba da gudanar da harkokin Masallacin su na Jami’urrahman.