Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina na cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara.
An ce maharan sun kuma kashe akalla mutane shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar Katsina.
Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin suke cin karensu babu babbaka, ba su fita ba har zuwa ranar Lahadi da rana.
Jaridar Aminiya ta yi hira da Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Gara na Ƙaramar Hukumar Funtua, in da ya bayyana cewa “Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ’yan mata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53.
- Gwamnonin APC Sun Kai Wa Muhammadu Buhari Ziyara
- Yan Sanda Sun Fara Binciken Kisan Gillar Da Aka Yiwa Matar Aure A Kano
“Sun kashe mutum a Layin Gara na Ƙaramar Hukumar Funtua da kuma wasu mutum biyu a garin Mai Kwama a cikin Karamar Hukumar Ɗandume,” in ji Malam Ya’u.
Shi ma maigarin Layin Gara, Mustapha Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutanensa na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, kwatsam kuma sai ga wannan matsala ta harin ’yan bindiga.
“Gwamnati tana ji tana gani wani abin ba a yi mana. Sojoji ma yadda ake turowa mu ba mu samu gatan an turo mana su ba, ’yan sandan da suka zo sai dai suka wuce suka nufi gardawa,” in ji Mustapha Abdullahi.
Kawo lokacin haɗa wannan rahoto Hukumar ’yan sanda a jihar ta Katsina ta ce tana kan bincike a kai lamarin, domin haka ba za ta ce komai ba sai ta kammala.
