• Home  
  • NUJ Ta Bukaci Rundunar Yan Sandan Nijeriya Ta Nemi Afuwa Kan Dukan Yan Jarida A Lokacin Zanga-zanga
- Babban Labari

NUJ Ta Bukaci Rundunar Yan Sandan Nijeriya Ta Nemi Afuwa Kan Dukan Yan Jarida A Lokacin Zanga-zanga

Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya NUJ, ta bukaci ‘yan sandan kasar da su nemi afuwa kan dukan da ‘yan sanda suka yi wa wasu ‘yan jarida a lokacin zanga-zangar da aka yi a ranar Litinin a wasu jihohin kasar. Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar na kasa Comrade Paul Bazia da kuma sakatariyar […]

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya magantu kan kai wa jami'ansa hari

Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya NUJ, ta bukaci ‘yan sandan kasar da su nemi afuwa kan dukan da ‘yan sanda suka yi wa wasu ‘yan jarida a lokacin zanga-zangar da aka yi a ranar Litinin a wasu jihohin kasar.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar na kasa Comrade Paul Bazia da kuma sakatariyar kungiyar Dr. Ijeoma Tubosia, suka fitar, kungiyar ta yi alawadai da matakin da wasu jami’an ‘yan sanda suka dauka na dukan ‘yan jarida inda ta bukaci a gaggauta gano su tare da hukuntasu.

Sanarwar ta ce,” Mu a matsayinmu na masu sanya idanu a cikin al’umma, ba zamu zauna muna gani ana aikata ba dai-dai ba sannan kuma mu yi shiru. A don haka abubuwan da ake sun isa haka duk wanda ya kara kai wa wani dan jarida hari to zai dandana kudarsa.”

Kungiyar ‘yan jaridun ta bayyana abin da ya faru da rashin tausayi da kuma take hakkin ɗan jaridar.

Cikin ‘yan jaridar da lamarin ya shafa akwai ma’aikacin gidan talbijin na Channels da Naija FM da Nigeria Info da na AIT da kuma na Super FM.

An watsawa ‘yan jarida hayaki mai sa hawaye a lokacin da suke bakin aiki a yayin zanga-zangar inda daga bisani kuma aka musu dukan tsiya tare da tsare su da jami’an tsaro suka yi.

Daga nan kungiyar ‘yan jaridar ta bayyana takaicinta a kan abin da ya faru, inda ta ce hukumar da aka kafa domin kare al’umma ta koma mai cin zarafin al’umma, musamman ƴanjarida a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Ta kuma gargaɗi rundunar ƴansandan kan cewa kada ta rusa kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninta da kafafen yaɗa labarai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai