Home » An samu karin farashin danyen mai a kasuwar duniya da faduwar darajar kudin Amurka

An samu karin farashin danyen mai a kasuwar duniya da faduwar darajar kudin Amurka

by Anas Dansalma
0 comment
Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya karu ranar Juma’a domin fatan da ake yi kan karin bukatar danyen mai da ake yi a China da kuma raunin da dala ke kara yi.

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya karu ranar Juma’a domin fatan da ake yi kan karin bukatar danyen mai da ake yi a China da kuma raunin da dala ke kara yi.

Da safiyar Juma’a dai an sayar da gangar danyen mai samfurin Brent kan dalar Amurka 75.80 maimakon dalar Amurka 75.67 da aka sayar da ita ranar Laraba.

Ita kuwa gangar danyen mai samfurin WTI an sayar da ita kan dalar Amurka 70.70 maimakon dalar Amurka 70.62 da aka sayar da gangarta a baya.

Fatan da ake yi cewa tattalin arzikin China zai sake farfadowa, wanda aka yi hasashen cewa zai sa danyen mai ya yi tsadar gaske, ya sake karuwa bisa ga irin yadda aka rarrage yawan kudin ruwa a kan bashi a kasar.

Sannan ma’aunin dalar Amurka, wadda ke auna darajar dalar Amurka idan aka gwada da darajar kudade irin su Yen din Japan da fan din Birtaniya da dalar Canada da Krona din Sweeden da Franc din Switzerland, ya fadi zuwa 101.668 da safiyar Juma’a.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?