Ɗaruruwan mata a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya, sun gudanar da zangazangar nuna ƙin amuncewa gwaje-gwaje da wasu jami’ai ke yi a yunƙurin gina wata katafariyar matatar man fetur a yankin.
Mata da dama ne suka zaɓi aske gashin kansu, wasu kuma suka yi yajin cin abinci, a wani mataki na nuna adawa da ƙudurin kafa matatar man.
‘Yan sanda sun sanya dokar hana zirga-zirga tare da amfani da kulake da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Haka zalika sun kama tare da tsare wasu mata ‘yan gwagwarmayar nuna adawa da gina matatar.