• Home  
  • An soke tashin jirgin sama saboda wani ƙaramin yaro da ya ƙi zaunawa
- Kasuwanci

An soke tashin jirgin sama saboda wani ƙaramin yaro da ya ƙi zaunawa

An soke tashin wani jirgin saman ƙasar Canada bayan wani ƙaramin yaro ya ƙi zama a kujerarsa tare da ɗaure bel a lokacin da za a tashi. Jirgin na kamfanin Porter Airlines na kan titin da zai tashi a filin jirgin sama na Victoria International Airport da ke British Columbia, lokacin da ma’aikatan jirgin suka […]

An soke tashin wani jirgin saman ƙasar Canada bayan wani ƙaramin yaro ya ƙi zama a kujerarsa tare da ɗaure bel a lokacin da za a tashi.

Jirgin na kamfanin Porter Airlines na kan titin da zai tashi a filin jirgin sama na Victoria International Airport da ke British Columbia, lokacin da ma’aikatan jirgin suka lura cewa yaron ya ƙi zama a kujerarsa.

Kamfanin jirgin ya ce iyayen yaron da ma’aikatan jirgin sun yi ta ƙoƙarin ganin an zaunar da yaro amma abin ya ci tura, inda daga bisani jirgin ya koma domin a sauke yaron da iyayensa tare da kayansu.

Saboda wannan jinkiri, jirgin ya fasa tashi saboda an rufe titin tashin jiragen saman da ƙarfe 12:30 na dare.

Hakan ya sa fasinjojin da ke cikin jirgin mai ɗaukar mutum 132, suka kwana a filin jirgin, maimakon su isa birnin Toronto. Ba a bayyana shekarun yaron ba, ko kuma adadin fasinjojin da ke cikin jirgin a lokacin.

Kamfanin ya nemi afuwar fasinjojin bisa abin da ya faru, tare da tabbatar da cewa an sake shirya musu wani jirgin da ya tashi washegari.

Dokokin jiragen sama na buƙatar fasinjoji su zauna a kujerunsu kuma su ɗaure bel musamman a lokacin tashin jirgi da saukarsa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai