Ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Pate, ya ce gwamnatin Najeriya ta ware wasu asibitoci 154 a faɗin ƙasar domin ba da kulawa ga masu juna biyu kyauta.
ya bayyana hakan a yayin wata tattauna da gidan talabijin na Channels.
Farfesa Pate ya ce waɗannan asibitoci za su kula da duk wata larura da ta shafi masu juna biyu kama daga lokacin da suke da juna biyun da lokacin haihuwa da bayan haihuwarsu wanda ke shafar uwa da kuma ɗan cikin nata.
Sannan ya ce wadannan asibitoci suna da isassun ma’aikata da inganci da kayan aiki na zamani wajen karɓar haihuwa.
“Gwamnati ta amince da ba wa masu juna biyu kulawa kyauta a wasu asibitoci da gwamnati ta ware kuma kulawar ta haɗa har dayin aiki kyauta,”
“Ba iya aiki na cire jariri ba har ma da ba da kulawa ga zubar jini da sauran larurori da suka shafi masu juna biyu. Idan mai juna biyu ta isa asibiti wanda yake da shaidar ba da irin wannan kulawa, gwamnati ce za ta biya wannan asibiti.”
Matsalolin lafiya na masu juna biyu na faruwa ne yawanci a lokacin da mace ke da juna biyu ko in ta zo haihuwa ko bayan haihuwa wanda ke shafar uwar ko ɗanta ko duk su biyun.
Waɗannan laurori ka iya sama ƙananan ko manya da kan yi barazana ga rayuwa idan ba a samu kulawar likitoci ba.
Wasu daga cikin irin larurorin da masu juna biyu ke fama da su sun haɗa da: hawan jini (preeclampsia) da yin naƙuda kafin cikar lokacin da ya kamata a yi (preterm labour) da wani nau’i na ciwon suga da ke kama masu juna biyu (gestational diabetes) da aikin yoyon fitsari.
Pate ya kuma jaddada cewa gwamnati ta himmatu wajen magance matsalar yoyon fitsari ta hanyar zaɓar cibiyoyin lafiya 18 da za su ba da kulawa kyauta a Najeriya.
Ya bayyana cewa, matsalar yoyon fitsari na shafar mata a ƙalla 10,000 a duk shekara wanda ke barinsu cikin mawuyacin hali na fama da yoyon fitsari da kan jawo tsangwama a cikin al’umma.
“Ana buƙatar aiki domin magance matalar wacce ke buƙatar ƙwarewa da kayan aikin duk da aiki ne mai tsada,” ya faɗa.
“An daɗe mata na fama da wannan larura ba tare da samun damar yi musu aiki ba. Mun shirya tsaf domin ganin duk macen da ke fama da wannan larura an yi mata aiki wanda gwamnati za ta biya.”
Ministan ya ce akwai kusan mata 2,000 da aka riga aka yi musu wannan aiki kuma abun tausayi ne ganin yadda suke ta godiya saboda samun damar buɗe sabon shafi a rayuwarsu.
Matsalar yoyon fitsari babbar damuwa ce ga ɓangaren lafiya a Najeriya musamman a yankunan karkara. Kuma wannan matsala na faruwa ne yawanci saboda shan wahala wajen naƙuda da auren wuri da rashin samun kulawar lafiya ingantacciya.
Ba wa lafiyar mata muhimmanci:
Pate ya jaddada cewa alfiyar al’umma da walwalarsu muhimmin abu ne ga gwamnatin shugaban Tinubu.
Sai dai ya ce la’akari da yawan mutuwar mata masu juna biyu ya sa gwamnati bai wa wannan matsala fifiko domin rage yawan mace-macen ta hanyar tabbatar da rashin kuɗi bai zama dalilin ƙara samun mutuwar wata mace ba saboda irin kulawar da za ta samu.
Pate ya ce wannan wani yunƙuri ne da gwamnati ke yi tare da haɗin guiwar hukumar inshoran lafiya ta ƙasa domin tabbatar da an bai wa lafiyar mata muhimmanci.
Sannan Ba wani abu ba ne sabo idan aka kalli yawan matan da suke mutuwa sakamakon juna biyu.
Majalisar ɗinkin duniya ta ce 1 cikin mutane 7 na mutuwar mata masu juna biyu yana faruwa ne a Najeriya wanda ya haura mata 50,000 da ke mutuwa a duk shekara.
Masana kiwon lafiya na ganin cewa kaso 95% na abin da ke jawo mutuwar mata masu juna biyu larurori ne da za a iya magance su.
A wani yunƙuri na magance matsalar mutuwar mata masu juna biyu, gwamnati a watan Nuwambar 2024 ta sanar da cewa CS ya zama kyauta ne ga masu juna biyu.
Sai dai ministan ya ce duk da wannan mataki, adadin mata masu juna biyu da ke mutuwa bai ragu ba, domin akwai an samu ƙananan hukumomi 172 da aka samu mutuwar mata masu juna biyu da ya kai sama da kaso 50% a Najeriya.
Pate ya ce haɗin guiwa tsakanin hukumar inshora lafiya (NHIA) da hukumar kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko, zai tabbatar da an samun kulawa marar yankewa ga mata masu juna biyu a Najeriya.