Mutane 21 ne suka jikkata yayin da wani mai suna Ibrahim Sani, dan shekaru 14 ya rasa ransa, sakamakon fashewar tukunyar Iskar gas, a gidan marigayi Sheik Isyaka rabi’u dake unguwar Goron Dutse Kano.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da Muhasa Radio, da misalin karfe 6:49 pm na yammacin ranar Litinin.
Sanarwar ta ce lamarin mara dadi ya faru ne da misalin karfe 2:30Pm na ranar Litinin, lokacin da tukunyar Gas din dake dakin dafa abinci ta yi bindiga sannan wutar ta watsu da ta sanadiyar mutuwar yaro dan shekaru 14 tare da jikkata wasu 21.
- An Ware Asibitoci 154 Domin Kulawa Da Mata Masu Ciki Kyauta A Najeriya
- An Kaddamar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaron Makarantu A Kano
bayan samun faruwar lamarin ne aka tura dakarun yan sanda karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan yan sandan Kano, dake kula Area Commander ta Dala, ACP Nuhu Mohammed Digi, inda suka yi gaggawar kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Dala Orthopaedic da kuma asibitin kwararru na Murtala Muhammed kano, don ci gaba da kula da lafiyarsu.
Rundunar yan sandan ta ce a kokarin jami’an ta tuni sun samu nasarar kashe wutar.
Kwamishinan yan sandan jihar ya yabawa jami’ansa da jami’an hukumar kashe gobara da al’ummar jihar bisa hadin kan da suka bayar wajen kashe gobarar .
A karshe rundunar ta jajanta wa iyalan wanda ya rasa ransa sanadiyar fashewar tukunyar gas, tare da yiwa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya.
- Yar Shekaru 14 Ta Nutse A Kogi A Kokarin Diban Ruwa
- NNPCL Ya Dakatar Da Yarjejeniyar Siyar Da Mai Da Naira