Home » An Kaddamar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaron Makarantu A Kano

An Kaddamar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaron Makarantu A Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Rundunar yan sandan Jihar Kano tare da hadin gwiwar rundunar yan sanda ta Nijeriya, sun fara gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan tsaron makarantun jihar, na wuni biyu, daga ranar Litinin 10 ga watan Maris zuwa Talata 11 ga watan Maris 2025

An  shirya taro ne don tattaunawa da kuma lalubo hanyoyin magance matsalolin da suke yi wa harkar ilimi tarnaki a fadin jihar , ta hanyar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da shugabannin kananan hukumomi, don tabbatar da tsaro a makarantu da suke kan iyaka da makotan jahohi.

Taron masu ruwa da tsakin ya hada gwamnan jihar Kano, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, hukumomin tsaron jihar, sarakunan gargajiya, malaman addini, wakilan kungiyoyin al’umma da kuma PCRC, don tattaunawa matakan kare makarantu.

CP Abayomi Shogunle PHD, fsi.

Da yake gabatar da jawabinsa Ko-odinetan bayar da tsaron makarantun daga shelkwatar rundunar yan sandan Nijeriya Abuja, CP Abayomi Shogunle, ya ce manufar yin wannan taron shi ne don su kara janyo jama’a jikinsu, domin aikin tsaro na kowa ne ba jami’an yan sanda kadai ba.

Haka zalika ya kara da cewa za su bayar da horo ga yan bijilanti da mafarauta tare da hada kai don tabbatar da tsaro a makarantun Nijeriya.

Dr. Ali Haruna Makoda

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin kwamishinan ma’aikatar ilimi Dr. Ali Haruna Makoda, ya jaddada  kudirin gwamnatin jihar na bayar da gudunmawar da ta kamata don inganta ilimin yara, ciki harda samar da na’urorin da za su taimaka don habbaka ilimi da tsaron dalibai a fadin jihar.

Gwamnan ya yabawa hukumomin tsaron jihar, bisa jajircewarsu na tabbatar da tsaro a koda yaushe, inda ya ce Kano tafi kowacce jiha zaman lafiya a Nijeriya.

Sheik Mallam Ibrahim Khalil

Shugaban majalissar malamai na jihar Kano, Sheik Malam Ibrahim Khalii , ya ce jami’an yan sanda suna da muhimmanci sosai ga rayuwar dan adam, harma ya shawarci mahukunta da su dinga samarsu da makwanci mai kyau su da iyalansu, domin a cewarsa duk lokacin da ake tattauna yadda za a samar da tsaro ana magana ne kawai kan makaman da ake bawa jami’an tsaron don gudanar da aiki.

AIG Ahmed Ammani

Anasa jawabin babban sufeton yan sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu Egbetokun, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa mai kula da shiya ta daya a jihar Kano, AIG Ahmed Ammani, ya ce duk lokacin da mutum yaji wani abu  ya sanar da su domin daukar matakan tsaro, kuma yan sanda a shirye suke , amma wajibi ne jama’a su taimaka musu da bayanan sirri.

Taron dai an yi masa take da kara karfafa kaimin jami’an tsaro don tabbatar da tsaro a makarantu.

A karshe rundunar yan sandan Kano ta ce za ta tabbatar da kowanne yaro ya samu damar samun ingantaccen ilimi cikin kyakkyawan yanayi.

PPRO Zone One, PPRO Kano Command

Farfesa Kamilu Sani Fagge

AIG Salman Dogo Garba

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?